Sauran Samarin Ki Sun Gaza Lyrics
- Genre:Amapiano
- Year of Release:2023
Lyrics
Yeah...
Dj Saniyaya
Sauran samarin ki sun gaza
In kinaso ki gane hakan soyayya dani ki gwada
(zo ki gwada ki gani)
Ki bani so kiga yanda ake gwada kauna
(yanda ake gwana kauna)
Ki kyale kowa kiyi ni kawai a nufi na
(soyayya)
Damuwar ki duk ta kare
Hawayen ki sai na share
Kula da lafiyar ki na dage
In adana kamar zinare
Fada in kinada bukata
In ma kudi kisa na fusata
Zanyi shela na furta sam zuciyar ki karda a bata ta
Na fada na nanata
Nifa na samo mata
Wacce bana haufi kowa ya ganta tsabar kyawun ta
Ni ke na gano
Har tarkona na dano
Jarumi na maza ne kan soyayya nafi rago
Sauran samarin ki sun gaza
Bazasu iya da rikon ki ba kyakkyawa babu yaudara
Aure nazo muyi dake ina fata
Sake ankara
A kanki na shirya bencha yan mata
Babu takura
Muyi auren kauna mu burge yan baya
Zamu burge kowa
Da an ganmu tunda mun dace
Babu juya baya
Amana ciko na kauna ce
Anyi dagiyar a rabamu
Amma dukan mu mun nace
Shifa so nakowa ne
Amma iya rikon shi sai wane
Dana fada da kin gane
Domin kuwa kina a raina ne
Banda damuwa domin kuwa mai tarbiya na samo
Zabi aka ban na dauki gyada ne na kyale bawo
Ai ko a gida akace mata kece zana kawo
Wacce bata yawo
Sai da na bincika na gano
Ko nai miki nisa toh ki sani dole zana dawo
Naji sanyi-sanyi
Yaki taho da sauri-sauri
Sonki naji Nabi
Ki gaya musu wallah ban barin ki
Sauran samarin ki sun gaza
Bazasu iya da rikon ki ba kyakkyawa babu yaudara
Aure nazo muyi dake ina fata
Sake ankara
A kanki na shirya bencha yan mata
Babu takura
Muyi auren kauna mu burge yan baya
Baby yar gata
Sauran samarin ki sun gaza
Hidimar da nake iya yi miki ba wanda zai iya